Shugaba Buhari ya yi alkawarin tallafawa sojojin dake mulkin Chadi

2

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya za ta tallafa wajen daidaituwar kasar Chadi da kuma tabbatar da komawarta bisa tsarin mulki.

Shugaban ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Abuja a lokacin da yake karbar bakuncin shugaba Mahamat Idris Deby na Chadi.

A cewar Shugaba Buhari, Najeriya ta san irin rawar da Chadi ta taka wajen taimaka mata a yaki da ta’addanci.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana mahaifin sabon Shugaban Chadin wato Idris Deby Itno a matsayin abokinsa kuma abokin Najeriya kuma Chad ta ba da kaimi wajen tsare Najeriya.

A jawabinsa, Janar Mahamat Idriss Deby ya godewa Najeriya bisa irin hadin kan da aka nuna musu bayan mutuwar mahaifinsa kuma tsohon shugaban kasar Chadi.

Marigayi Idris Deby ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji a wata fafatawa da yan tawaye a watan Aprilu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − six =