Ma’aikatan shari’ah sun bayar da sharadin janye yajin aiki

1

Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta kasa dake yajin aiki, ta yi watsi da kudirin da gwamnonin jihoshi 36 suka gabatar don aiwatar da yancin cin gashin kai na bangaren shari’ah da ma’aikata ke nema.

Gwamnonin, a cikin kudirin nasu, suna neman a kirkiro Kwamitin Rabon Kudaden Jiha domin kula da rabon kudade ga bangarorin gwamnati uku a matakin jiha.

Amma a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar bayan zaman ganawar ranar 8 ga Mayu na kwamitin ayyukanta na Kasa, kungiyar ta dage kan bukatarta cewa dole ne a cire kudaden bangaren shari’ah kai tsaye daga asusun tarayya kuma a biya shugabannin kotuna ta hanyar Hukumar Shari’a ta Kasa.

Ta kafe kan cewa baza a iya sauya abubuwan da kundin tsarin mulki ya tanada ba, saboda haka dole ne a bi su.

A matsayin sharadin kawo karshen yajin aikin da take yi, kungiyar kwadagon ta dage kan cewa dole sai an cire dukkan bangaren shari’ah na watan Oktoba 2020 zuwa Mayu 2021 kai tsaye daga asusun tarayya, kuma a biya shugabannin kotunan ta hanyar Majalisar Shari’a ta Kasa kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + fifteen =