Gwamnatin Kaduna da kungiyar kwadago sun cimma yarjejeniya

8

Gwamnatin Jihar Kaduna da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun cimma matsaya akan shirin gwamnatin jihar na korar ma’aikata daga aiki.

Kungiyar ta NLC tun ranar Litinin ta jagoranci ma’aikata domin zanga-zangar adawa da shirin gwamnatin jihar na korar ma’aikata.

Gwamnatin tarayya ce ta samar da maslaha wajen cimma yarjejeniyar tsakanin bangarorin biyu jiya a Abuja.

Wani bangaren yarjejeniyar shine gwamnatin jihar Kaduna zata kiyaye wajen bin ka’idoji a shirinta na garanbawul ga aikin gwamnati, wanda aka sa ran zai haifar da rage yawan ma’aikata.

Bangarorin sun kuma amince cewa kungiyar ta NLC baza ta cigaba da yajin aiki ba kuma babu wani ma’aikaci da gwamnatin jihar za ta hukunta saboda ya shiga yajin aikin.

Gwamnatin jihar Kaduna tunda farko ta sanar da korar daruruwan malaman jami’o’i da ma’aikatan jinya wadanda suka shiga yajin aiki.  Kuma nan gaba kadan ake sa ran za a janye wannan sanarwar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − one =