Gwamnatin Tarayya ta shirya gurfanar da ‘yan Boko Haram 800

18

Kimanin mutane 800 ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram aka shirya gurfanarwa a gaban shari’ah da zarar an janye yajin aikin ma’aikatan shari’a.

Mutanen 800 na daga cikin wadanda ake zargi kimanin dubu 1 wadanda masu gabatar da kara a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya suka yi nazarin bayanansu.

Yanzu haka wadanda ake zargin suna tsare a hannun sojoji a Maidugurin jihar Borno.

Wata Mataimakiyar Darakta a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da ke Abuja, Chioma Onuegbu, wacce ke aiki a sashen gabatar da kararraki na ma’aikatar, ta sanar da haka a Abuja a wajen wani horo da aka shiryawa ’yan jarida.

A cewar Chioma, daga cikin kararraki kusan dubu 1 da aka bibiya,800 daga cikinsu suna da gamsasshiyar shaida don cigaba da shari’a, yayin da aka bayar da shawarar sakin 170 saboda rashin shaida.

Ta kara da cewa daga cikin kararraki 800 dake da gamsasshiyar shaida, an shigar da 280 daga cikinsu a gaban kotu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − three =