Mutane 20 sun mutu sanadiyyar cutar Kwalara a Bauchi

7

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa cutar amai da gudawa ta kashe akalla mutane 20 a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aliyu Maigoro ne ya bayyana hakan a yau a wani taron manema labarai da ya kira a hedikwatar ma’aikatar da ke Bauchi.

Yace kananan hukumomi 9 a jihar sun samu jimillar mutane 322 da suka kamu da cutar a wata daya inda ya kara da cewa yawan mace-macen ya kai kashi 6.2 cikin 100.

Yace ma’aikatar ta hannun Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta hanzarta kai dauki don hana yaduwar cutare zuwa sauran kauyuka da unguwanni, inda ya kara da cewa an gano cewa akwai bullar irin wannan cuta a karamar hukumar Sumaila dake makotaka da sauran Kananan Hukumomin Jihar Kano.

Aliyu Maigoro ya ce tuni aka kaddamar da cibiyoyin kula da cutar kwalara guda hudu a cikin garin Bauchi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da Asibitin Kwararru na Bauci, da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matasa da kuma Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko dake Kandahar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 3 =