An saki daliban Islamiyya 11 a Neja

7

Gwamantin jihar Neja ta ce an saki dalibai 11 cikin kusan 150 da wasu ‘yan bingida suka sace lokacin da suka kai hari kan wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina.

Wasu ganau sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun sace gwamman daliban makarantar Salihu Tanko Islamic School, koda yake sun saki wasu daga cikin daliban saboda kanana ne.

A cewar shaidun, ‘yan bindigar sun rika harbi kan mai-uwa-da-wabi kafin daga bisani su dauke daliban.

Sai dai cikin wata sanarwa da gwamantin jihar ta fitar ta ce an harbi mutane biyu lokacin harin kuma an tabbatar da mutuwar daya daga ciki, yayin da guda ke cikin mawuyacin hali. Kazalika gwamnatin ta ce tana cigaba da tattara bayanan tsaro kan harin, kafin daga bisani ta dauki matakan da suka dace.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − 3 =