Gwamna Matawalle ya dakatar da Sarkin Dansadau

10

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya amince da dakatar da Mai Martaba Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar, nan take.

Gwamna Matawalle ya kuma amince da nadin Hakimin Dansadau, Alhaji Nasiru Muhammad Sarkin Kudu, a matsayin wanda zai kula da harkokin masarautar.

Cikin wata sanarwa da mai bashi shawara na musamman akan wayar da kai, kafafen yada labarai da sadarwa, Mallam Zailani Baffa, Gwamnan ya kuma dakatar da Hakimin Nasarawa Mailayi, Alhaji Bello Wakkala, nan take.

Gwamnan ya amince da kafa wani kwamiti mai karfi domin binciken ayyukan masu sarautar gargajiyar da aka dakatar a Dansadau da Nassarawa Mailayi.

Gwamna Matawalle ya kuma sake tabbatar da umarnin da fadar shugaban kasa ta bawa hukumomin tsaro na harbin dukkan wani mutum da aka gani dauke da bindiga.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − 14 =