Gwamna Matawalle ya rushe majalisar zartarwa

8

Gwamnan Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rushe majalisar zartarwarsa nan take.

Gwamnan ya kuma tumbuke sakataren gwamnatin jihar, Bala Bello Maru da shugaban ma’aikata, Kanal Bala Mande, mai ritaya.

Daga cikin wadanda lamarin ya shafa akwai dukkan shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin daban-daban.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bawa gwamnan shawara na musamman akan wayar da kan jama’a, kafafen yada labarai da sadarwa, Zailani Baffa.

Rushewar bata shafi hukumomin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kafa su ba.

Sanarwar ta umarci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar ayyukan ma’aikatunsu ga manyan sakatarorinsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 + 18 =