Tsagin APC a Jigawa yayi watsi da dakatar da Gudaji Kazaure

4

Tsagin shugabannin jam’iyyar APC a karamar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa ya bayyana dakatarwar da aka yiwa dan majalisar wakilai ta tarayya, Muhammad Gudaji Kazaure, a matsayin abinda ya sabawa doka.

Gudaji Kazaure yana wakiltar Kazaure da Roni da Gwiwa da Yankwashi a majalisar wakilai ta tarayya.

Tsagin shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar, a wata wasika ta ranar 31 ga watan Mayu wacce aka aikawa kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta APC na kasa, ya bayyana hukuncin da aka yanke akan dan majalisar da cewa ya sabawa doka.

Kamar yadda yazo a wasikar, tsagin jam’iyyar yayi ikirarin cewa ‘ya’yan jam’iyyar guda 4 ne kacal suka dakatar da Gudaji Kazaure.

Kazalika, makale jin wasikar, akwai sa hannun da adireshin wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar.

Wasikar, wacce ke dauke da sa hannun jagoran shugabannin jam’iyyar APC na Kazaure, Bello Sanda, ta bayyana cewa kashi 2 cikin 3 na shugabannin jam’iyyar a karamar hukumar na goyon bayan dan majalisar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five − 4 =