Ana gudanar da zaben ‘yan majalisa a Aljeriya duk da kiran kauracewa

3

Ana gudanar da zaben ‘yan majalisa a kasar Aljeriya, wanda wasu jiga-jigan wata tafiyar zanga-zanga suka kauracewa kuma mutane da dama ke yiwa zaben kallon na jeka na yi ka ne.

Tangal-tangal na mulkin siyasa da faduwar farashin danyen mai, kari bisa annobar corona sun lalata sauye-sauye dayawa da gwamanti tayi alkawari, wacce ta dare mulki bayan gagarumar zanga-zangar da ta tursasawa shugaban kasa sauka daga mulki a shekarar 2019.

Yan takarkarun da basu da jam’iyya dayawa sun shiga zaben sosai fiye da kowane lokaci a baya, kuma a karon farko a zaben kasar Aljeriya, mata ne rabin ‘yan takarkarun.

Ana sa ran samun sakamakon zaben a ranar Litinin mai zuwa.

Wannan shine zabe na uku da aka yi a kasar da tafi kowace girma a Afirka tun bayan da shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika yayi murabus a watan Aprilun 2019.

Wanda ya gaje shi, Abdelmajib Tebboune, yace wannan zaben zai jawo ballewa daga gwamnati mai rashawa tare da kafa harsashin sabuwar kasar Aljeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 15 =