Buhari yace gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10.5 daga talauci

8

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta fitar da mutane miliyan 10 da rabi daga kangin fatara da talauci. Shugaban kasar ya fadi haka a yau a jawabinsa na ranar demokradiyya.

Ya lissafa manoma da kananan ‘yan kasuwa da masu aikin hannu da mata ‘yan kasuwa, daga cikin mutanen da rayuwarsu ta inganta a karkashin mulkinsa.

Shugaban kasar ya kuma ce gwamnatinsa tana bisa turba wajen cika alkawarinta na fitar da mutane miliyan 100 daga cikin kangin talauci.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi gwamnoni da jawowa kasarnan wahala sanadiyyar yajin aikin kungiyar ma’aikatan shari’ah ta kasa.

A lokacin da ya karbi bakuncin majalisar shiga tsakanin addinai ta kasa jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja, shugaban kasar yayi magana dangane da jajircewarsa wajen mayar da ragamar mulki ga hannun jama’a.

Shugaban kasar ya kuma yi jawabi dangane da illar yajin aikin, inda ya jajanta matsalar da ya jawo kan harkokin tsaro.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daidaikun mutanen da suka dauki nauyin ta’addanci a sassan kasarnan daban-daban, sun yi haka ne saboda a cigaba da damawa da su.

Shugaban kasar ya bayyana haka a jiya a wata fira da aka yi da shi a gidan talabijin na NTA.

Buhari, wanda yake amsa tambayoyi dangane da mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci, wadanda gwamnatinsa ta kama ‘yan kwanakinan, ya bayyana cewa dayawa daga cikinsu masu arziki ne wadanda a yanzu basa cikin gwamnati.

Yace za a hukunta wadannan mutane a gaban shari’ah.

Kimanin yan kasuwa 400 ne, cikin har da ‘yan chanji, aka cafke a yan kwanakinan bisa zargin suna daukar nauyin Boko Haram.

Har yanzu babu wanda aka taba yankewa hukunci a kasarnan bisa daukar nauyin Boko Haram, kungiyar data jawo mutuwar gomman dubban mutane a Arewacin kasarnan tun daga shekarar 2009.

A wani cigaban kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kyakykyawan fatan cewa kasarnan zata shawo kan matsalolin dake addabarta a halin yanzu.

Shugaba Buhari, a jawabin da ya yiwa ‘yan kasa a yau domin ranar demokradiyya, yace kasarnan a cikin shekaru 2n da suka gabata ta fuskanci, tare da shawo kan wasu manyan kalubale wadanda ka iya tarwatsa sauran kasashe musamman masu alaka da tsaro.

Kazalika, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace jam’iyyar APC za ta cigaba da kasancewa akan mulki har sai illah ma sha Allahu.

Shugaban kasar ya fadi haka a jiya a wata fira da aka yi da shi a gidan talabijin na kasa (NTA).

Yace an yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta ginu sosai. Shugaban kasar ya kuma sha alwashin cewa bazai cigaba da mulki ba muddin wa’adinsa ya kare.

Shugaban kasar ya bayyana sha’awar da yake da ita ta mika kasar bayan ta cigaba, ga magajinsa a shekarar 2023.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + 7 =