Buhari ya sha alwashin dawo da zaman lafiya a jihar Borno

12

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari jiya a Maidugurin Jihar Borno ya tabbatarwa da ‘yan jihar kokarin gwamnatin tarayya wajen kawo karshen yaki da Boko Haram, tare da tabbatar da cewa ‘yan gudun hijira sun koma rayuwarsu ta yau da kullum, inda ya yabawa Gwamna Babagana Zulum bisa juriyarsa da kokarinsa wajen sake gina jihar.

Shugaba Buhari a wata ziyarar aiki zuwa jihar domin duba yanayin tsaro tare da kaddamar da wasu ayyuka, ya danganta nasarorin da sojoji ke samu a ‘yan kwanakinnan akan masu tayar da kayar baya a garuruwan Dikwa da Damboa da Gwoza da shirye-shirye masu kyau da samar da sabbin makamai da kayan yaki tare da shugabancin sojoji nagari.

Shugaban Kasar yace dukkan manyan hafsoshin soji da aka nada a bana sun taba yin aiki a matsayin kwamandojin yakin Boko Haram.

Shugaban Kasar yace marigayi Shugaba Idris Deby na kasar Chadi ya taka muhimmiyar rawa a yaki da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, inda ya umarci magajinsa da yayi aiki tukuru wajen mayar da kasar mulki demokradiyya tare da tallafawa kokarin dawo da zaman lafiya a yankin.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya yayi bayanin nasabarsa ta haihuwa inda yace duk da kasancewarsa Fulani, amma mahaifiyarsa tana da alaka da Kanurin jihar Borno.

Shugaba Buhari ya sanar da haka a fadar Shehun Borno a lokacin ziyarar aikin da ya kai jiya zuwa jihar.

Shugaban Kasar wanda ya isa Maiduguri da safe, ya kaddamar da ayyuka bakwai da suka hada ganin manyan makarantu da kananan asibitoci.

Ana sa ran zai mayar da martani bayan Gwamna Babagana Zulum da Shehun Borno sun kammala jawabansu.

Amma akan ya mayar da martani dangane da matsaloli da bukatun da suka mika masa, shugaban kasar sai ya koma tarihi inda yake sanar da nasabarsa da ayyukansa ga gwamnati. Tunda farko, Shehun Borno wanda ya dauki dogon lokaci yana jinjinawa shugaban kasa bisa kaunarsa da mutanen Borno, yayi amfani da wannan damar wajen rokon shugaban kasar ya taimakawa jihar ta dawo da yan gudun hijira daga arewacin Borno zuwa garuruwansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 7 =