Sojoji da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Kenya

16

Dakarun sojin Kenya sun tabbatar da mutuwar sojoji dayawa bayan wani jirgin soji mai saukar ungulu ya fado a lokacin atisaye a wajen Nairobi, babban birnin kasar.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa da dakarun sojin ta fitar.

Sai dai, sanarwar sojojin bata bayar da adadin yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Sanarwar ta kara da cewa an dauke sojojin da aka jikkata zuwa wani asibitin sojojin dake Nairobi.

Har yanzu babu cikakken bayani dangane da yawan sojojin dake cikin jirgin amma kafafen yada labaran birnin sun ce sojoji 23 ne.

Dakarun sojin sunce masu binciken hadarin jiragen sama sun isa wajen da jirin ya fado domin gano musabbin hadarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 + four =