Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen karuwar GDP da kashi 4.2 a 2021

1

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen kididdigar abinda take samar wa a shekara wato GDP zai karu da kashi 4.2 cikin 100 a shekara mai zuwa.

Ministar Ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Hajiya Zainab Ahmed, ta sanar da haka a jiya a wajen tattaunawa akan kundin kasafin na matsakaicin zango daga shekarar 2022 zuwa 2024.

Zainab Ahmed tace GDP wanda aka yi hasashen zai karu da kashi uku cikin 100 a bana, an rage shi zuwa kusa da kashi 2.5 cikin 100.

Ministan ta cigaba da cewa hasashen GDP na badi shine naira tiriliyan 184 da biliyan 380, kari daga naira tiriliyan 168 da biliyan 600 a bana, daga nan kuma zuwa naira tiriliyan 201 a shekarar 2023 da naira tiriliyan 222 a shekarar 2024.

Ta kuma ce ana sa ran alkaluman hauhawar farashi ya sauko kadan zuwa kashi 13 cikin 100 a badi daga kashi 15 cikin 100 a bana.

Ta yi nuni da cewa an samu hauhawar farashin kayayyaki ne saboda faduwar darajar Naira.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =