Yanzu-Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar

17
Muhuyi Magaji

Majalisar dokokin jihar kano a yau Litini ta dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasahawa da karban korafe-korafe na jihar Kano, Barr Muhuyi Magaji Rimin-gado daga mukaminsa har na tsawon wata daya, sakamakon kin amincewa da akawun da aka tura zuhu hukumarsa daga ofishin akanta na jihar Kano.

A baya dai, anyi rade-raden cewa dangantaka tayi tsami tsakanin Muhuyi da gwamna Ganduje sakamakon wani bincike da Muhuyi keyiwa wasu daga iyalan Gwamnan.

Dakatar da shugaban hukumar hana cin hanci da rashawar tazo ne bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta karbi takardan korafin akansa daga ofishin babban akanta na jihar Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 2 =