HAƊAKAR ƳAN UKU A SIYASAR JIHAR KANO: WACCE MANUFA SU KA SANYA A ZABEN 2023 ?

4

Daga Bashir Abdullahi El-bash

-Guguwar Ƴan Uku Ta Taso Da Ƙarfi Daga Yankin Kano Ta Kudu.
-Sun Haɗu Akan Manufa Ɗaya Bisa Yarda Da Taimakekeniyar Cimma Burukan Siyasa.
-Idan Su Ka Ɗore A Haka, Da Wuya Wani Tsagin Siyasa Ya Iya Samun Galaɓa A Kansu Duba Da Gogewa Da Tasiri Da Yawan Mabiya.

A daidai lokacin da zaɓen siyasar 2023 ya ke cigaba da kusantowa, ƴan siyasa su na cigaba da ƙulle-ƙullen siyasa na fili da na ƙarƙashin ƙasa domin neman cimma buri. Siyasar Jihar Kano ta na ɗaya daga cikin siyasu masu zafi da ɗaukar hankali da buƙatar shiri na gaske ga ƴan siyasa masu neman matsayi a kowane mataki.

Ƙila wannan dalili shi ne ya haifar da haɗakar manyan ƴan siyasa daga yankin Kano ta Kudu a wannan zaɓe su ka haɗe wuri ɗaya kan manufa da shiri domin cimma burukan da su ka sanya a gaba. 

Ƴan ukun su ne: Ɗan majalissar ƙasa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa (Sardaunan Rano) sannan shi ne shugaban masu rinjaye na majalissar. Da tsohon kakakin majalissar dokokin Jihar Kano sannan ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Rano, Bunkure da Kibiya, Hon. Kabiru Alhassan Usman Rurum (Turakin Rano). Da tsohon ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Sumaila da Takai, Hon. Suleman Abdurrahman Kawu Sumaila, (Turakin Sumaila). Dukkansu sun fito ne daga Kudacin Kano.

Wannan haɗuwa tasu ta na da alaƙa ne da burin da su ke da shi na son samun ɗan takarar gwamna daga wannan yanki nasu na Kano ta Kudu a 2023, sannan hasashe ya yi nuni da cewa tsohon kakakin majalissar Jihar Kano, wakilin Bunkure, Rano da Kibiya, Alhassan Rurum shi ne wanda sauran biyun su ka yi wa juna alƙawarin marawa baya domin ya samu takara har ya kai ga samun nasarar lashe zaɓen.

Idan wannan buri nasu ya cika Rurum ya samu takarar gwamna, su na kuma da buri da alƙawari da juna cewa Hon. Ado Doguwa shi ma za su yi duk mai iyuwa domin ganin ya sake komawa kan kujerarsa ya kuma samu nasarar zama shugaban majalissar wakilai ta ƙasa gaba ɗaya.

Hon. Kawu Sumaila, burinsu ya zama Sanatan Kano ta Kudu. Kamar yadda wasu su ka sani Kawu Sumaila tsohon ɗan majalissar tarayya ne, sannan tsohon ɗan takarar sanata kuma tsohon ɗan takarar gwamna a wannan Jiha. A yanzu haka wannan haɗaka ta ƴan uku ba su da wani burin da ya wuce su ga Kawu ya zama Sanata 2023.

A dunƙule waɗannan ƴan uku hasashe ya yi nuni da sun yarda da juna sun kuma amincewa juna za su yi aiki tare bisa amana domin cimmawa kai waɗannan buruka na siyasa 2023, idan har ba su kai ga samun nasarar samu ɗan takarar gwamna ba daga cikinsu akwai iyuwar su marawa ɓangaren mataimakin gwamna Dakta Gawuna baya bisa yarjejeniyar za a ba su mataimakin gwamna. Kuma dama can tare su ke da juna a fannin siyasar.

Wannan haɗaka ta ƴan uku za a iya cewa barazana ce ga duk wani mai neman kujerar gwamna a Jihar Kano idan aka yi duba da muƙamansu da tasirinsu da yawan mabiyansu. Misali; yau a Jihar Kano idan aka cire Kwankwaso da Shekarau, Kawu Sumaila zai iya zuwa na uku a yawan mabiya da ƙarfin faɗa aji.  Allah ya yi masa ƙarfin zuciyar alheri da temakawa mutane wanda hakan ya ba shi farin jini da karɓuwa sosai ga jama’a.

Haka duk in kaɗauke su za ga su na da karɓuwa a wurin mutane su na amfani da damarsu wajen gina matasa. Gaba ɗayansu Ƴan siyasa ne da su ka yi ƙarfi, su na da kuɗi su na da yawan mabiya, sun san duk wani loko da kusurwar ƙullin siyasa. Duba da wannan haɗewar tasu za ta iya kai su ga cimma burin da su ka nufa, idan har su ka ɗore a haka to fa za a iya cewa gobara ce daga kogi maganinta sai dai Allah kawai da wuya wani tsagin siyasa ya yi nasara a kansu.

Bashir ya rubutu wannan ra’ayin nasa ne daga jihar Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 6 =