TA YAYA GWAMNA GANDUJE ZAI SAMAR DA SULHU DA ZAMAN LAFIYA MAI ƊOREWA A TSAKANIN ƁANGARORIN MUSULMAI DA KE FAƊA DA JUNA A JIHAR KANO ?

2

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

“Haramun Ne Musulmi Ya Yi Gaba Da Ɗan Uwansa Musulmi Sama Da Kwana Uku”. Cewar Manzon Allah S.A.W.
-“Yin Sulhu A Tsakanin Mutane Biyu Masu  Saɓanin Da Juna, Aiki Ne Wanda Ya Fi Sallah Da Sadaka, Da Azumi”. Inji Manzon Allah S.A.W.
-“Duk Wanda Ya Samar Da Sulhu A Tsakanin Ɓangarori Biyu Domin Neman Yardar Allah, Za Mu Ba Shi Babban Sakamako”. (An-Nisaa:14).

Kamar yadda aka yi muƙabala a tsakanin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malamai na ɓangarorin ƙungiyoyin addinin musulunci na ɗarika da tijjaniyya da izala kuma su ka yi nasara akansa har ma haɗin kai ya wanzu a tsakanin su Malaman ɗarikar da izalar da tijjaniyar, sannan Abduljabbar ɗin ya yi nadama, to a fahimtata abu na gaba da ya kamata mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya maida hankali a kai a yanzu shi ne samar da wani sulhun a tsakanin Abduljabbar ɗin da yayansa duba da tsawon lokacin da su ka ɗauka ba sa ga maciji da juna.

Mai girma gwamna kowa ya sani mutum ne mai son haɗin kai da zaman lafiyr al’umma, sannan shugaba ne mai haƙuri da tawali’u da rungumar kowa babu bambanci, kowa nasa ne. Waɗanda su ke aibata shi ma fahimtarsa ne ba su yi ba, amma a hankali idan aka cigaba da tafiya a haka, na tabbata kowa zai fahimci dattakunsu da ƙaunarsa ga zaman lafiya da haɗin kan musulmai. Ina fatan mai girma gwamna zai haɗa kan manyan masu faɗa aji daga malamai da attajirai wajen haɗuwa da samar da sulhu a tsakanin waɗannan ƴan uwan juna tare da duk wasu masu faɗa aji da ke da saɓani da juna a wannan jiha domin mai girma gwamna baban kowa ne a dukkan faɗin Jihar nan. 

Matakan da ake bi wajen samar da sulhu da gina zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin al’ummar musulmai da ke taƙaddama da juna, a tsare ya ke cikin manhajar koyarwar addinin Musulunci. A wurare daban-daban cikin alƙur’ani mai girma da hadisan manzon Allah S.A.W an nuna muhimmancin ƴan uwantaka da kwaɗaitar kan muhimmancin shiga tsakanin ɓangarori biyu waɗanda su ke gaba da juna domin yin sulhu a tsakaninsu. 

A alƙur’ani mai girma, Allah ya faɗa cewa: “Musulmai ba komai ba ne face ƴan uwan juna, saboda haka ka samar da zaman lafiya a tsakanin ƴan uwanka biyu ka kuma kiyayi Allah zai kiyaye ka cikin rahamarsa”. (Al-Hujaraat:10).
Manzon Allah S.A.W ya ce: shin ba na faɗa muku wani abu wanda ya fi azumi ya fi sallah ya fi sadaka ba ?, Sai su ka ce: “Na’an. Sai ya ce: “Sulhu a tsakanin mutane biyu kan wani saɓanin da su ke da shi da juna wanda ka ya haifarwa da ruɗani cikin addini”. (Al-Tirmidhi-Hasan).

A takaice, ƙarya haramun ce a addinin Musulunci, amma a fannin sulhu, Allah ya amince ya yarda wani ya shirya ƙarya ya faɗa a ƙoƙarin yi wa mutane masu saɓani da juna sulhu, domin kaucewa rigima da tashin hankali. Domin gaba da saɓanin mutane ya kan haifar da fitina cikin addinin mutum da na al’umma gaba ɗaya.

Ummu Khalthoom ta faɗa cewa ta jiyo manzon Allah S.A.W ya na cewa: “Ba maƙaryaci ba ne wanda ya daidaita tsakanin mutane ta hanyar faɗa musu daɗaɗan kalamai da abu mai kyau”. (Al-Bukhari, Muslim).

Ta kuma ƙara da cewa:  “Ban ji wasu wurare da manzon Allah S.A.W ya amincewa mutane su yi ƙarya ba face sai akan abubuwa uku kamar haka: akan yaƙi, da abin da miji zai faɗawa matarsa, ko abin da mata za ta faɗawa mijinta wajen yabon juna da kuma wajen ƙoƙarin sulhunta mutane”. (Muslim).

Yin sulhu a tsakanin ɓangarori guda biyu, na nufin samun babban sakamako. Allah Ya faɗa cewa: “Babu wani mai kyau cikin keɓantacciyar hirarsu face ga wanda ya ba da sadaka da kyawawan ayyuka ko ya samar da kykkyawa a tsakanin mutane. Duk wanda ya yi haka kan neman yardar Allah, za mu ba shi babban sakamako”. (An-Nisaa:14).

Duk yadda ake, a ya yin samar da zaman lafiya a tsakanin ɓangarori biyu, a tuna cewa Musulunci ya na da hanyoyi da tsarin magana kan wannan batu. Ba batu ne na sauƙi ba “magance rikici”. Ba za mu samar da daidaito cikin sauƙi ba har sai mun kai ga samar da yarjejeniya a tsakaninsu gaba ɗaya. A matsayinmu na musulmai, mu sanya Allah farko, mu yi wa kowane ɓangare adalci”.

A madadin nazarin matsayin ɓangarorin biyu kan alaƙarsu da juna, akwai buƙatar mu duba kowanne kan alaƙarsu da Allah, kowane mutane za su iya saɓawa da juna amma bai zama lallai sun saɓa ne akan hanyar Allah ba. Dan haka, duk waɗanda su ka saɓa ana kiransu ne a kan hanyar Allah. Allah Ya ce:
“Idan ɓangarori guda biyu na masu imani su na rigima, ku samar da daidaito a tsakaninsu. Sannan idan wani ɓangaren ya bijire ya koma yaƙar ɗaya ɓangaren to ku yaƙe wanda duk ya bijire har sai ya dawo kan hanyar Allah. Idan har ya dawo ɗin to ku yi mai kyau bisa daidaito da adalci a sakaninsu. Tabbas, Allah Ya na son masu adalci”. (Al-Hujaraat:9).

Dan haka, ba su kaɗai ba, ya mai girma gwamna, duk waɗanda su ke jayayya, ba sa magana da juna, ko su ke rigima da sauran musulmai, matuƙar an san su kuma su na da tasiri cikin al’umma, to aje a same su a yi musu sulhu. Ka yi hakan domin neman yardar Allah, ka tuna da falalarsa ka kuma roƙe shi ya karɓa daga gare ka. Ba wai za ka samu sakamako ba ne kaɗai daga gare shi, hakan zai kasance ɗaya daga cikin manyan ayyuka masu daraja da ka yi.

Ali Ibn Abi Talib ya ce: ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo gafara shi ne sanya farin ciki a zukatan sauran musulmai. Anas kuma ya ce: “Duk wanda ya samar da zaman lafiya a tsakanin ɓangarori biyu, Allah zai ba shi duk wani sakamako da zai tserar da shi“.

Abu Umama ya ce: “Ka yi tafiyar mil domin ziyartar marar lafiya, sannan ka yi tafiyar milamilai domin ziyartar ɗan uwanka kan neman yardar Allah ka kuma yi tafiyar mil uku domin yi wa ɓangarori masu saɓani sulhu.
Addinin musulunci ba ya son musulmai su kasance masu rikici da rigima da faɗa da juna. Musulunci ya koyar da mantawa da bambance-bambance a tsakanin juna domin kaucewa tsana da ƙyamar juna waɗanda ka iya haddasa fitina su rusa addinin da al’ummar. 

Idan har ya zama dole sai musulmi ya yi gaba da musulmi, to addinin musulunci iya kwanaki uku ya ƙayyade musulmi ya ƙauracewa musulmi cikin mu’amalar zamantake ko magana da juna. Bayan kwanaki uku wajibi ne duk mai gaba da wani ya mance a yi wa juna afuwa a cigaba da mu’amala.

Manzon Allah S.A.W ya faɗa cewa: “Ka da ka ƙauracewa wani, ka da ka yi gaba da wani, ka da ka tsani wani, ka da ka yi hassada ga wani. Ka kasance bawan Allah ɗan’uwan kowa. Ba a yarda wani musulmi ya ƙauracewa wani musulmi sama da kwana uku ba”. (Bukhari, Muslim).

Sannan kuma: “Duk wanda ya kauracewa ɗan uwansa tsawon shekara kamar ya na shanye jininsa ne“. Abu Dawud, Saheeh Al-Baani”.

A saboda haka ina shawartar mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje (KHADIMUL ISLAM) ya yi ƙoƙarin tsamowa al’ummarsa daga halaka, ya kafa kwamiti mai ƙarfi domin yi wa waɗannan ƴan uwa da sauransu mutane masalaha. A fahimci abin da ya jawo rikicin a kuma nazarci kowane ɓangaren da abin da za a iya yi masa ya daidaita da ɗayan domin ɗinke al’ummar musulmai wuri ɗaya a samu cigaba a yaƙi da fitintinu cikin addini da al’umma Jihar Kano da duniyar musulunci su zauna lafiya.

Allah Ya yaye gaba da ƙyashi da hassada da ƙiyayya a tsakanin musulmai. Allah Ya ba mu ikon so da ƙaunar junanmu.

El-Bash ya rubutu wannan ra’ayin nasa ne daga jihar Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 5 =